Najeriya na shirin takaita yawan al'ummar kasar
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwmnatin Najeriya ta bayyana shirinta na rage yawan al’ummar kasar ta hanyar kayyade wa mata haihuwa kamar yadda Ministar Kudi, Zainab Ahmed ta sanar.
Ministar wadda ke magana a gefen taron tattalin arziki a birnin Abuja, ta ce, a halin yanzu, gwamnatin na ganawa da sarakunan gargajiya da suka ki amincewa da wannan mataki a can baya saboda dalilai na addini da al’ada.
A cewar Ministar, za a dauki matakin ne don tunkarar kalubalen farfado da tattalin arziki da kuma aiwatar da shirin gwamnati na takaita yawan ‘yan kasar.
Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraron kalaman Ministar Kudin Najeriya kan takaita haaihuwa.
Kalaman Ministar Kudi kan takaita haihuwa a Najeriya
A yayin zantawa da RFI Hausa, Kasim, Kurfi masanin tattalin arziki a Najeriya, ya ce, akwai hanyoyi da dama na magance matsalar tattalin arziki, amma mawuyaci ne wannan shirin ya cimma nasara a Najeriya a cewarsa.
Kasim Kurfi kan hanyar magance talauci a Najeriya
Yawan al’ummar Najeriya ya habbaka daga miliyan 45.1 da ake da shi bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960 zuwa kusan miliyan 200 a bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu