Najeriya

Wadanda ake zargi da hallaka Janar Alkali sun mika kansu

Motar Janar Alkali mai ritaya da aka tsamo daga wani kududdufi a yankin DU dake karamar hukumar Jos ta kudu.
Motar Janar Alkali mai ritaya da aka tsamo daga wani kududdufi a yankin DU dake karamar hukumar Jos ta kudu. Daily Trust

Uku daga cikin mutane bakwai da rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta yi shelar nema ruwa a jallo sun mika kansu, sa’o’i 24 bayan fitar da sanarwar, bisa zarginsu da hannu wajen kisan gillar da aka yiwa Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya.

Talla

Mutanen da suka mika kan nasu ga jami’an tsaron sun hada da Dagacin yankin Du dake karamar hukumar Jos ta Kudu Yakubu Rapp; shugaban matasan yankin Matthew Rwang da kuma wani direban motar daukar yashi Timothy Chuwang.

A wani labarin kuma rundunar sojin Najeriyar ta sanar da gano wani kabari da ake kyautata zaton a nan aka binne tsohon jami’in nata bayan hallaka shi, kafin daga bisani ya tone shi daga ciki.

Yayin da yake karin bayani kan lamarin, Manjo Janar B.A Akinruluyo yace sun samu nasarar gano kabarin mara zurfi ne bayan da wasu majoyoyi har kashi hudu suka nuna musu, daga bisani kuma, aka yi amfani da karnuka wajen tabbatar da zargin.

A ranar 3 ga watan satumban da ya gabata manjo janar Idris Alkali mai ritaya ya bace, kwana guda bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan yankin na DU dake Jos ta Kudu.

Hakan ya sanya rundunar sojin Najeriya kaddamar da bincike domin gano babban jami’in nata da ya bace, inda aka gano motarsa da wasu karin guda biyu cikin wani kududdufi dake yankin na DU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.