Najeriya

Gwamnoni sun gaza cimma matsaya kan batun karin albashi

Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari a tsakiyar wasu takwarorinsa.
Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma Gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari a tsakiyar wasu takwarorinsa. Sahara Reporters

Gwamnonin Najeriya sun gaza cimma matsaya dangane da bukatar kungiyar kwadagon Najeriya ta neman karin Albashi, bayan taron da suka yi a wannan Litinin a garin Abuja.

Talla

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo da kuma sakataren gwamnatin tarayyar kasar Boss Mustafa.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma Gwamnan jihar Zamfara AbdulAzeez Yari ya jaddada cewa gwamnoni, baza su iya biyan karin Albashin ba, sai dai gwamnan yace a ranar Talata, 30 ga watan Oktoba mai karewa, za su sake gudanar da taro domin yanke shawara ta karshe dangane da batun.

Gwamnan Zamfara AbdulAziz Yari kan batun karin albashi

A ranar 24 ga watan Oktoba, kungiyar Kwadagon Najeriya NLC ta yi barazanar sake shiga yajin aikin sai baba ta gani, saboda gazawar gwamnatin Najeriya, wajen amincewa da bukatarta ta karin mafi karancin albashin ma’aikata zuwa naira dubu 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.