Najeriya

Toshon jigo a PDP Tony Anenih ya rasu

Marigayi Cif Tony Anenih
Marigayi Cif Tony Anenih Daily Trust

Tsohon Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP kuma tshon Ministan Ayyuka da Gidaje a Najeriya, Cif Tony Anenih ya rasu yana da shekaru 85.

Talla

Majiyoyi sun tabbatar da mutuwarsa a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Abuja bayan fama da gajeren rashin lafiya.

A cikin watan Julin da ya gabata ne, Anenih wanda ake yi wa kirari da “Mr. Fix It” ya bayyana cewa, ba zai gudanar da bikin ranar haihuwarsa karo na 85 cikin shagulgula ba saboda asarar rayukan da aka samu a kasar.

Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu fitattun ‘yan siyasar kasar suka aika da sakon ta’aziya ga iyalan mamacin dan asalin jihar Edo.

Ana saran sanar da jana’izarsa nan gaba kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.