Bakonmu a Yau

Farfesa Usman Yusuf Shugaban hukumar Inshorar Lafiya ta NHIS kan makomar matakin dakatar da shi

Sauti 04:08
Farfesa Usman Yusuf Shugaban hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya NHIS.
Farfesa Usman Yusuf Shugaban hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya NHIS. Daily Post Nigeria

Sakataren Gwamnatin Najeriya Boss Gida Mustapha ya bayyana cewar babu wata hukumar gudanarwar gwamnati dake da hurumin dakatar da shugaban hukumar da shugaban kasa ya nada.Mustapha ya bayyana haka ne sakamakon takaddamar da ta kaure tsakanin shugaban hukumar inshoran lafiya ta NHIS da kuma shugabannin gudanarwar ta.Yanzu haka dai shugaban Prof Usman Yusuf na cigaba da gudanar da ayyukan sa kamar yadda aka saba.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban hukumar Inshorar Lafiyar ta NHIS kan dakatarwar kuma ga tsokacin da yayi akai.