Najeriya

Gwamnoni na taro karo na 2 kan karin albashi

Wasu daga cikin gwamnonin jihohin Najeriya yayin gudanar da wani taro a Abuja kan batun karin mafi karancin albashi.
Wasu daga cikin gwamnonin jihohin Najeriya yayin gudanar da wani taro a Abuja kan batun karin mafi karancin albashi. Daily Post Nigeria

A wannan Talata Gwamnonin Najeriya ke gudanar taro zagaye a karo na biyu domin cimma matsaya kan batun karin albashin ma’aikata.

Talla

Kungiyar Gwamnonin ta NGF ta ce tilas ne dukkanin ‘ya’yanta na jihohi 36 su halarci taron na yau ba tare da tura wakilci ba.

Baya ga dukkanin gwamnonin jihohin Najeriyar, taron zai kuma samu halartar sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da Ministar Kudi Zainab Ahmed, da kuma Ministan kwadago Chris Ngige.

Taron gwanonin na yau ya zo ne bayan sa’ao’i 24 da gudanar da makamancinsa a ranar Litinin da ta gabata, inda suka gaza yanke shawara kan batun na karin albashi.

A gefe guda kuma, duk dai a wannan Talata, kwamitin lura da tattalin arzikin Najeriya da ke karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo, zai gana da kungiyar gwamnonin, domin cimma matsaya guda dangane da karin mafi karancin albashin ma’aikata.

A ranar 24 ga watan Oktoba, kungiyar Kwadagon Najeriya NLC ta yi barazanar sake shiga yajin aikin sai baba ta gani, saboda gazawar gwamnatin Najeriya, wajen amincewa da bukatarta ta karin mafi karancin albashin ma’aikata zuwa naira dubu 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.