Bakonmu a Yau

Kwamishinan ‘Yan Sanda Ahmad AbduRahman kan rikicin jihar Kaduna

Sauti 03:43
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya yayin aikin sintiri a jihar Kaduna.
Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya yayin aikin sintiri a jihar Kaduna. REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana matukar bacin ran sa kan yadda Jihar Kaduna ta koma dandalin tashin hankali, inda ya bayyana cewar duk wanda aka samu da hannu a rikicin bayan bayan nan zai gamu da fushin hukuma.Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Jihar domin ganawa da shugabannin ta, da kuma jajanta musu kan asarar rayukan da aka yi.Bayan kammala ziyarar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar ta Kaduna Ahmad Abdurrahman, wanda yayi karin bayani kan halin da ake ciki.