Najeriya

'Yan Sanda sun kama mabiya akidar Shi'a 400

Yan Sandan Najeriya, sun tarwatsa taron mabiya akidar Shi'a.
Yan Sandan Najeriya, sun tarwatsa taron mabiya akidar Shi'a. REUTERS/Abraham Achirga

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da kama mabiya akidar Shi’a sama da 400 bayan kazamar arangamar da suka yi a birnin Abuja, wanda ya kai ga jikkata mutane da dama.

Talla

Kwamishinan ‘yan sandan birnin na Abuja, Bala Ciroma ne ya sanar da haka, yayin gabatar da wadanda aka kama a hedikwatar ‘yan sandan kasar.

Kwamishinan yace an kama mabiyan akidar ta Shi’a ne, sakamakon tarzomar da suka haifar, zalika an kwace muggan makamai daga hannunsu, wadanda suka kunshi, kwalabe 31 dauke da fetur da ake yin amfani da su wajen haddasa gobara, da sauran abubuwa masu hadari.

Dangane da wannan lamari wakilinmu daga Abuja, Muhammad Sani Abubakar ya aiko mana da rahoto.

'Yan Sanda sun kama mabiya akidar Shi'a 400

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.