Najeriya

Kashe 'Yan Shi'a a Najeriya ya saba wa doka- Amnesty

Wasu mabiya akidar Shi'a a Najeriya
Wasu mabiya akidar Shi'a a Najeriya guardian.ng

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da kisan da Sojojin Najeriya suka yi wa wasu mabiya akidar Shi’a da ke tattakin zanga-zanga a gefen birnin Abuja.

Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Amnesty ta ce, ga alama, Sojojin Najeriya na amfani da wasu dabaru da aka kitsa da gan-gan don kashe ‘Yan Shi’a a yayin taronsu.

A cewar sanarwar, binciken Amnesty ya nuna cewa, Sojoji da Jami’an ‘Yan sanda da suka yi amfani da karfin da ya wuce kima sun kashe ‘Yan Shi’a akalla 45 a cikin kwanaki biyu.

Amnesty ta ce, Jami’anta sun halarci wurare daban-daban guda biyar a Abuja da jihar Nasarawa don ganawa da mabiya Shi’ar da ke karbar magani sakamakon raunin da suka samu a tashin hankalin.

Amnesty ta zanta da wadanda lamarin ya shafa da kuma shaidun gani da ido har ma jami’an kiwon lafiya baya ga tantance hotunan wadanda aka kashe a yayin zanga-zangar wadda aka gudanar a ranakun Asabar da Litinin.

A cewar Amnesty, ta gane wa idanunta yadda Sojojin da ‘Yan sanda suka yi amfani da karfin da ya wuce kima kan mabiya shi’ar, abin da ya saba wa dokokin Najeriya da kuma na kasa da kasa a cewar Darektan Amnesty a Najeriya, Osai Ojigho.

Ojigbo ya ce, Jami’an Tsaron sun harbi ‘yan shi’ar a sassa daban daban na jikinsu da suka hada da wuya da kai da baya da kirji da kafada da kafa da kuma hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.