Najeriya

"Gwamnatin Najeriya na shirin dankwafar da yajin aikin gama-gari"

Wasu mambobin NLC a Najeriya
Wasu mambobin NLC a Najeriya NLC

Gamayyar Kungiyoyin Kwadagon Najeriya ta zargi gwamnatin kasar da shirin dankwafar da ayyukanta gabanin tsunduma cikin yajin aikin game gari a ranar Talata don tilasta wa gwamnatin biyan Naira dubu 30 a matsayin karancin albashin ma’aikata.

Talla

Gamayyar ta kuma yi watsi da ganawa da gwamnatin a cikin daren da ya gabata don cimma wata sabuwar matsaya game da batun karancin albashin, in da daukacin shugabanninta suka kaurace wa zama da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Shugabannin Kungiyoyjn sun jaddada cewa, babu makawa, za a gudanar da wannan yajin aikin na sai baba-ta gani, yayin da suka ta bukaci sauran kugiyoyin fararen hula da su mara musu baya don ganin sun cimma burinsu na ganin an yi adalci a biyan albashin.

NLC da TUC da kuma ULC duk sun shawarci ‘yan Najeriyar da ba za su shiga cikin tawagar za ta yi tattakin zanga-zangar lumana a ranar Talata ba, da su zauna a gidajensu don kauce wa shiga mawuyacin hali.

Sai dai Kungiyoyin na zargin gwamnatin ta bullo da dabaru da dama da suka hada da dabarar “ babu aiki, babu albashi” don dankwafar da gudanar da yajin aikin.

Koda yake bangaren gwamnatin ta bakin Ministan Kwadago, Dr. Chris Ngige ya musanta yunkurin dankwaafar da yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.