Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Ra'ayoyin masu sauraro kan takaddamar neman karin albashi a Najeriya da kuma matakin shiga yajin aiki

Wallafawa ranar:

Kamar yadda watakila kuka ji a labaran duniya, bayan kwashe tsawon watanni na kokarin cimma yarjejeniya, yanzu haka Kungiyoyin Kwadagon Najeriya sun cimma matsaya da gwamnatin kasar kan mafi karancin albashin ma’aikata.Menene ra’ayoyinku kan tsawon lokacin da aka dauka na cece-kuce tsakanin bangarorin biyu kan wannan batu?Ko kuna ganin cewa, shugaba Buhari zai amince da dogon yajin aiki a dai dai lokacin da zabe ke karatowa?Shin kuna ganin yajin aiki na taka muhimmiyar rawa wajen magance wasu matsalolin rayuwa a kasashe daban-daban.Kan wannan al’amari shirin Ra’ayoyin ku masu sauraro ya baku damar tofa albarkaci a wannan rana kamar yadda Zainab Ibrahim ta gabatar.

Wasu 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya tare da shugabanninsu.
Wasu 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya tare da shugabanninsu. REUTERS/Akintunde Akinleye