Najeriya

INEC ce ta kayar da ni a zaben 2015- Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan tare da wasu manyan baki a bikin kaddamar da littafinsa a Abuja.
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan tare da wasu manyan baki a bikin kaddamar da littafinsa a Abuja. guardian.ng

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi bayyana cewa, Hukumar Zaben Kasar da Farfesa Attahiru Jega ya jagoranta ta taimaka wajen rashin tazarcensa a zaben 2015.

Talla

Jonathan na Jam’iyyar PDP ya amince da shan kayi a fafatawar da ya yi da shugaba Muhammadu Buhari a wancan lokaci, kuma a karon farko kenan a tarihin Najeriya da wani shugaba da ke kan ragamar mulki ya amince da kayin da jam’iyyar adawa ta yi masa.

A cikin littafinsa mai taken “My Transition Hours” da ya kaddamar a ranar Talata a birnin Abuja, Jonathan ya ce, bangarncin da INEC ta dauka wajen rabar da katunan zabe, ya yi sanadin rashin samun nasararsa a 2015.

A cewar Jonathan, katunan da INEC ta rabar da su a yankin arewaci da kuma arewa maso gabashin Najeriya mai fama da rikicin Boko Haram, sun zarce wadanda ta rabar a kudancin kasar duk da cewa, yankin ya fi arewacin zaman lafiya.

Kazalika tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana tsohon shugaban Amurka Barack Obama da wasu tsirarun ‘yan siyasa da suka kwaye masa baya a matsayin wadanda suka taka rawa wajen kashin da ya sha a zaben na 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.