Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta lashe gasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika karo na 9

'Yan wasan Najeriya mata Super Falcons bayan lallasa Afrika ta Kudu a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika.
'Yan wasan Najeriya mata Super Falcons bayan lallasa Afrika ta Kudu a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika. Pulse.ng
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Tawagar ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya ajin mata Super Falcons, tayi nasarar lashe kofin gasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika da Ghana ta karbi bakunci.

Talla

Karo na tara kenan da Super Falcons ke lashe kofin gasar nahiyar Afrikan ajin mata.

An dai fafata wasan karshe ne tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, inda Najeriyar ta samu nasara da kwallaye 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan kammala mintuna 90 da karin lokaci suna fafatawa a matsayin canjaras, 0-0.

Kafin wasan karshen, Najeriya ta lallasa Kamaru da kwallaye 4-2 a damar bugun daga kai sai mai tsaron gida, a zagayen wasan kusa dana karshe.

A halin yanzu Najeriya ta samu tikitin wakiltar nahiyar Afrika a gasar cin kofin duniya ajin mata da za ta gudana a kasar Faransa cikin shekara mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.