Najeriya

Muna sa ido kan ayarin mutanen da suka shiga Sokoto - 'Yan sanda

Wasu makiyaya a yankin Guana, dake wajen birnin Bamako, na Mali. 5/11/2016.
Wasu makiyaya a yankin Guana, dake wajen birnin Bamako, na Mali. 5/11/2016. REUTERS/Adama Diarra

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce tana ci gaba da sa ido kan ayarin wasu mutane da ake yada jita-jitar cewa gungun mayaka masu da'awar Jihadi ne suka cikin jihar Sokoto.

Talla

Wasu bayanai dai sun ce mayakan sun soma karbar haraji daga mazauna wasu yankunan karamar hukumar Tangaza dake jihar ta Sokoto.

Sai dai yayin da take karin bayani akan rahoton, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ayarin mutanen da suka shiga jihar mayaka ne.

Wakilinmu daga jihar ta Sokoto yana dauke da karin bayani a wannan rahoto da ya aiko.

Rahoto kan ayarin mutanen da suka shiga jihar Sokoto

Babbar jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Sokoto Cordelia Nwawe ta shaidawa manema labarai cewa bayan gudanar da bincike, sun gano cewa ayarin mutanen da aka firgita da su, makiyaya ne daga kasar Mali, wadanda basu shigo Najeriya domin tashin hankali ba.

A cewar rundunar ‘yan sandan makiyayan sun saba zuwa Najeriya domin kiwo, sai dai a wannan karon sun shigo kasar ce tare da dabbobin da yawansu ya zarta na lokutan baya.

Rahotanni sun nuna cewa a baya makiyayan na zuwa ne da akalla dabbobi dubu daya ko kasa da haka, amma a wannan karon yawan dabbobin ya kai akalla dubu uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI