Sarkin Zamfaran Anka Attahiru Ahmad kan tsaro a Zamfara da kafa kungiyar matasa ta ‘Jarumai da Gora’

Sauti 04:15
Wasu matasa a Najeriya na kungiyar sa kai ta Civilian JTF, da suka sadaukar da kansu wajen yakar masu tada kayar baya.
Wasu matasa a Najeriya na kungiyar sa kai ta Civilian JTF, da suka sadaukar da kansu wajen yakar masu tada kayar baya. News Express Nigeria

Gwamnatin Jihar Zamfara dake Najeriya ta kaddamar da wata kungiyar matasa da ake akira ‘Jarumai da Gora’ da zasu dinga taimakawa wajen aikin samar da tsaro a Yankunan su, sakamakon tabarbarewar al’amura a Jihar.Wannan ya biyo bayan kiraye kiraye daga shugabanni domin ganin an kara dabarun magance wannan matsala da tayi sanadiyar rasa rayukan daruruwan mutane a Jihar.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sarkin Zamfaran Anka Attahiru Ahmad, wanda kuma shima shugaban Sarakunan Jihar Zamfara baki daya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.