An bai wa Nuhu Ribadu lambar girma kan yakar rashawa a Najeriya
Wallafawa ranar:
An gudanar da wani bikin karrama mutanen da suka ba da gudunmawa wajen yaki da cin hanci da rashawa a sassa daban-daban na duniya. Bikin wanda ya gudana yau Juma'a a kasar Qatar ya yaba da irin gudunmawar da daidaikun mutane ke bayarwa wajen fatattakar ayyukan cin hanci da Rashawa cikin al'umma.
Kyautar wadda aka kasa ta a matakai daban daban ta duba irin gudumawar da jami’ai ke bayarwa wajen dakile yaduwar cin hanci da ke yi wa hukumomi illa da kuma tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin.
Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban Hukumar EFCC da ke Najeriya na daya daga cikin wadanda aka bai wa lambar girma na nuna gwarzantaka wajen yaki da cin hancin saboda rawar da ya taka a baya.
Bikin ya gudana a karkashin Sarkin Qatar, Sheikh Tamim Bin Hammad al Thani da Firaministan Malaysia Mahathir Mohammed da kuma Babban Daraktan ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da safara kwayoyi Mr Yuri Fedoyov.
Lambar girmar na dauke da tukucin Dala 250,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu