Najeriya

Amnesty:Ya kamata a zurfafa bincike kan rikicin Boko Haram

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, yayin cin abinci a wata cibiyar yi musu rijista a filin wasa na Geidam. 6/5/2015.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, yayin cin abinci a wata cibiyar yi musu rijista a filin wasa na Geidam. 6/5/2015. REUTERS/Afolabi Sotunde

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta bukaci kotun duniya ICC da ta kaddamar da bincike mai fadi kan manyan laifukan tauye hakkin dan adam da aka aikata a rikicin Boko Haram.

Talla

Yayin gabatar da bukatar ga kotun ta ICC, Amnesty ta zargi hukumomin Najeriya da gazawa wajen yanke hukunci kan bangarori, ko wadanda aka samu da aikata laifukan na cin zarafin dan adam yayin yakin Boko Haram.

Idan za’a iya tunawa, a shekarar 2010, babbar mai gabatar da kara ta kotun duniyar, Fatou Bensouda, kaddamar da wani binciken sharar fage kan rikicin na Boko Haram.

Binciken sharar fagen a waccan lokaci dai ya shafi bangarorin laifukan yaki da na cin zarafin dan adam guda 8 ne yayin rikicin.

Shidda daga cikin bangarori takwas na laifukan sun shafi mayakan Boko Haram ne, wadanda suka kunshi, yiwa fararen hula kisan gilla, satar dubban mutane, kaiwa makarantu da wuraren Ibada hare-hare, cin zarafin mata ta hanyar fyade, sai kuma amfani da kananan yara wajen kai harin kunar bakin wake, ko kuma a matsayin soji.

Sauran bangarori 2 na laifukan yakin kuwa, kotun ta ICC na zargin sojin Najeriya ne da aikata su wadanda suka kunshi, kai hari kan fararen hula, kame mutane masu yawa, da kuma tsare su ba bisa ka’ida ba.

Kotun ta duniyar na kuma zargin sojin Najeriyar da cin zarafin wadanda ke tsare a hannunsu, da kuma aiwatar da hukuncin kisa akan wasunsu ba tare da zuwa kotu ba.

A watan Oktoba na shekarar bara, aka soma gudanar da shari’un mutane 1,669 a jihar Niger, bayan shafe tsawon lokaci suna tsare, bisa zargin alakarsu da Boko Haram, kuma zuwa yanzu an zartas da hukunci kan akalla 113, na tabbatar da alakarsu da Boko Haram, yayinda aka sallami wasu 1,054.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI