Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan matakin Buhari na kin sa hannu akan sabuwar dokar zaben Najeriya

Sauti 03:51
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Darren Ornitz/File Photo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yaki sanya hannu kan sabuwar dokar zaben da Majalisun kasar suka amince da ita domin gudanar da zaben shekara mai zuwa.Buhari ya shaidawa shugabannin Majalisar cewar, ganin lokaci ya kure, kuma an fara gudanar da zaben shekara mai zuwa a karkashin dokar 2015, sanya hannu kan sabuwar dokar zai haifar da rudani da kuma shari’u a kotuna.Kan wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin shari’a Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na jami’ar Abuja.