Wasanni

Najeriya na gaf da samun tikitin gasar kwallon yashi ta Duniya

Najeriya ta lallasa Tanzania a gasar kwallon kafar kan yashi ta nahiyar Afrika.
Najeriya ta lallasa Tanzania a gasar kwallon kafar kan yashi ta nahiyar Afrika. Pulse.ng/CAF

Najeriya ta samu nasarar kaiwa zagayen kusa da na karshe a gasar kwallon yashi ta nahiyar Afrika bayan lallasa Tanzania da kwallaye 4-2 a ranar Litinin.

Talla

Yayin sauran wasannin da aka fafata a ranar ta Litinin, mai masaukin baki Masar ta lallasa Madagascar da kwallaye 4-2, yayinda Morocco ta samu nasara kan Ivory Coast da kwallaye 5-4.

A yau Talata za’a tantance sauran kasashe uku da za su kai zagaye na kusa dana karshe a gasar kwallon yashin, inda za’a fafata tsakanin Masar da Ivory Coast, Madagascar da Morocco sai kuma Senegal da za ta fafata da Libya.

Kasashe biyu da suka samu nasarar kaiwa zagayen wasan karshe ne za su wakilci nahiyar Afrika a gasar kwallon kafar kan yashi da kasar Paraguay za ta karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI