An zargi 'Yan Jaridun Najeriya da fifita siyasa fiye da komai
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An zargi ‘yan Jaridun Najeriya da mayar da hankali kan labarun siyasa maimakon janyo hankalin gwamnati da jama’a wajen ayyukan raya kasa da kuma haifar da cigaban al’umma.
Wata kungiyar ci gaba da ta duniya da ake kira Rebooth ta shirya taro na musamman ya janyo manema labarai da kuma 'Yan Jaridu domin tunatar da su kan nauyin da ya rataya akan su.
Wasu daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi yayin taron sun kalubalanci 'Yan Jaridu da su rika mayar da hankali kan fannonin ci gaban al'umma kamar sha'anin wutar lantarki, da sauran batutuwan tattalin arziki, a maimakon maida hankali kan siyasa fiye da komai.
Wakilinmu daga Abuja, Muhammad Sani Abubakar ya aiko da rahoto akan taron.
An zargi 'Yan Jaridu da fifita sha'anin siyasa fiye da komai
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu