Najeriya

'Yan takarar mataimakin shugaban Najeriya sun tafka muhawara

Mataimakin shugaban Najeriya  Farfesa Yemi Osinbajo, a tsakiyar sauran 'yan takarar kujerar mataimakin shugaban Najeriya yayin muhwarar da suka tafka a Otal na Transcorp Hilton dake Abuja.
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, a tsakiyar sauran 'yan takarar kujerar mataimakin shugaban Najeriya yayin muhwarar da suka tafka a Otal na Transcorp Hilton dake Abuja. YouTube

An soma tafka muhawara tsakanin ‘yan takarar kujerar mataimakin shugaban Najeriya a zaben 2019 da ke tafe, wadda aka soma a Otal din Transcorp Hilton dake Abuja.

Talla

A kashin farko na muhawarar, an fafata ne tsakanin ‘yan takara 5, da suka hada da Mataimakin shugaban Najeriya mai ci Farfesa Yemi Osinbajo daga jam’iyyar APC mai mulki, Khadijah Abdull-Iya daga ANN, da kuma Peter Obi na babbar jamiyyar adawa ta PDP.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Ganiyu Galadima dake yiwa Jam’iyyar ACPN takarar mukamin na mataimakin shugaban kasa, da kuma Umma Getso ta jam’iyyar YPP.

Batun tattalin arziki, da ya hada da samar da ayyukan yi, ababen more rayuwa, bunkasa da noma da kuma matsalolin tsaro ne suka mamaye muhawarar ta jiya.

Daya daga cikin muhimman batutuwan da mataimakin shugaban Najeriya mai ci Farfesa Yemi Osinbajo ya yi tsokaci akai, shi ne ragowar kudaden tallafin saukaka farashin mai da ya ce gwamnati za ta ci gaba da fitarwa duk da sukar hakan da ‘yan adawa ke yi.

A cewar Osinbajo, muddin gwamnati ta karasa cire ragowar kudin tallafin baki daya, to fa sai dai ‘yan Najeriya su rika sayen litar mai kan farashin naira 220 ko kuma sama da haka.

A nasu bangaren dai ‘yan takarar jam’iyyun adawar, sun zargi gwamnati mai ci da gazawa wajen cika alkawuran da ta yiwa ‘yan Najeriya.

Sauran muhimman batutuwan da ‘yan takarar jam’iyyun adawar suka soki gwamnatin APC sun kunshi halin kunci da ‘’yan gudun hijira ke ciki a arewa maso gabashin Najeriya, da kuma karfafa ilimin yara mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI