Najeriya

EFCC za ta cafke masu sayen kuri'u a zaben 2019

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, INEC Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, INEC Farfesa Mahmud Yakubu Ventures Africa

Hukumar Zaben Najeriya, INEC za ta yi aikin hadin guiwa da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC da kuma wasu hukumomin tsaro wajen dakile matsalar sayen kuri’u a zaben 2019.

Talla

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a wata zantawa a birnin Legas, in da ya ce, za su dauki matakin ne da zummar karya lagwan bata-garin ‘yan siyasa masu sayen kuri’u a lokutan zabe.

Farfesa Yakubu ya kara da cewa, ba za a amince wa masu kada kuri’u shiga rumfunan zabe da wayoyin salula na zamani ba duk dai da zummar tabbatar da ingantaccen zabe da ‘yan Najeriya za su yi madalla da shi.

Wannan na zuwa ne a yayin da shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu kan kudirin yi wa dokar zaben kasar kwaskwarima, abin da ya sa ‘yan adawa suka alakanta matakin Buharin da yunkurin jam’iyyar APC na shirya makarkashiyar lashe zaben na badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI