Najeriya

'Yan sandan Najeriya sun zama karnukan APC- In ji PDP

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta ce, tana aikinta yadda ya kamata
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta ce, tana aikinta yadda ya kamata Reuters

Jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Sokoton Najeriya ta zargi jami’an ‘Yan Sandan kasar da zama karnukan farautar abokiyar hamayyarta wato APC, bayan ‘Yan sandan sun cafke mata mutane bisa zargin su da daukar nauyin ‘yan dabar siyasa.

Talla

PDPn ta ce, Jami’an ‘Yan sandan sun sha keta hakkokin magoya bayanta ta hanyar kai musu hari har ma da kashe su, amma babu wani mataki da aka dauka kan lamarin duk kuwa da korafin da PDPn ta shigar wa Hukumar ‘Yan Sanda.

To sai dai jam'iyyar APC ta ce, ba ruwanta a ciki lamarin kuma zargin da PDP ke yi mata ba gaskiya ba ne, a yayin da ‘yan sandan ke cewar suna aikinsu ne yadda ya kamata.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren cikakken rahoton da Faruk Yabo ya aiko mana daga Sokoto kan wannan dambarwar.

PDPn dai ta cire tsammanin samun adalci dangane da ayyukan ‘yan sandan kasar baki daya.

Wannan na zuwa ne a yayin da jam’iyyun siyasa daban daban ke ci gaba da yakin neman zabe a sassan kasar gabanin babban zaben 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.