Najeriya

Hisbah ta kama masu auren jinsi a Kano

Jami'an Hisbah a jihar Kano na tabbatar da bin dokokin addinin Musulunci
Jami'an Hisbah a jihar Kano na tabbatar da bin dokokin addinin Musulunci RFI Hausa

Jami’an Hukumar Hisbah da ke tabbatar da bin dokokin Shari’ar Musulunci a jihar Kano da ke Najeriya, sun kama wasu ‘yan mata 11 bisa zargin su da shirin gudanar da bikin auren jinsi guda.

Talla

Hukumar ta Hisbah ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jami’anta sun kame ‘yan matan ne a ranar Litinin, yayin da suke tsaka da kammala shirin bikin auren jinsin.

Daraktan hukumar ta Hisbah Abba Sufi ya ce, cikin wadanda aka kama har da ‘yan matan da ke daukar kansu a matsayin mata da miji, abin da ya ce, babu tantama haramun ne a addinin Musulunci da kuma dokokin Najeriya da suka fayyace matakin a matsayin laifi babba.

Sufi ya ce, da zarar an kammala bincike za a gurfanar da ‘yan matan a gaban kotu.

Sai dai wata majiya daga hukumar ta Hisbah ta rawaito cewa ‘yan matan sun musanta zargin da ake musu, in da suka ce manbobi ne a wani Klob na rawa, kuma suna shirya biki ne domin taya ‘yar uwarsu murna da aka bai wa mukamin mataimakiyar shugabarsu.

Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar Hisbah ke irin wannan kame a jihar Kano, in da a shekarar 2007, ta kame wasu mata biyar bisa zargin su da bikin auren jinsi guda, wanda guda daga cikin su ta auri sauran matan guda hudu.

Sai dai ko a waccan lokacin, matan sun musanta zargin, in da suka yi ikirarin shirya bikin domin taya daya daga cikinsu murnar aure da za ta yi.

A watan Janairun shekara ta 2015 ma, jami’an Hisbah sun taba kama wasu matasa maza 12 a wajen birnin Kano bisa zargin su da shirya auren jinsi, zargin da suka musanta tare togaciyar cewa bikin murnar zagayowar ranar haihuwa suka shirya.

Kulla alaka ko auren jinsi guda, laifi ne da ake yankewa hukuncin kisa a jihohi 12 na arewacin Najeriya da ke bin tsarin shari’ar Musulunci, ko da yake zuwa yanzu ba a kai ga zartas da shi ba.

A shekarar 2014 kuwa, Majalisun Najeriya suka amince da dokar haramta auren jinsi tare da fayyace hukuncin daurin akalla shekaru 14 kan duk wanda aka samu da aikata laifin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI