Najeriya

Najeriya ta zargi Amnesty da tafka kura-kurai a rahotanta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Afolabi Sotunde

Gwamnatin Najeriya ta zargi kungiyar Amnesty International da wallafa rahoto cike da kura-kurai, wanda cikinsa ta bayyana gazawar gwamnati wajen daukan matakan da suka dace kan hare-haren ‘yan bindiga da suka yawaita cikin shekaru uku da suka gabata zuwa yanzu.

Talla

Kafin martanin na gwamnatin Najeriya, rundunar sojin kasar ce ta soma yin watsi da rahoton na Amnesty, tare da bukatar janyewarta daga cikin kasar bayan wallafa rahoton zargin sojin kasar da tauye hakkin dan adam musamman a yakin da ta ke yi da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Yayin mayar da martani na baya bayan nan, kakin shugaban Najeriya Garba Shehu, ya yabawa kungiyar ta Amnesty kan wasu batutuwa da ta tabbatar a cikin rahoton nata, wanda suka kunshi cewa, rikicin manoma da makiyaya a kasar ba shi da alaka da addini, sai kuma cewa wasu bata garin ‘yan siyasa ne suke rura wutar haddasa rikicin domin cimma wasu manufofi, abinda shugaba Buhari ya sha jaddadawa.

Sai dai a cewar Garba Shehu, akwai bayanai da dama da kungiyar ta Amnsety ta tafka kura-kurai wajen tattara su.

Kakakin shugaban Najeriyar, ya ce ba gaskiya bane bayanin Amnesty da ke nuna rikicin manoma da makiyaya sabon abu ne da ya bijiro shekaru 3 da suka gabata, domin kowa ya san cewa matsala ce da ke nan sama da shekaru 100 da suka gabata, kuma turawan mulkin mallaka sun adana bayanai kan rikicin na waccan lokaci.

Garba Shehu ya kara da cewa gwamnati ta dauki matakan kawo karshen rikicin da kuma gudanar da bincike kan zarge-zargen tauye hakkin dan adam, kuma ba shakka an samu sauki kan rikicin, sabanin yadda kungiyar ta Amnesty ta wallafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI