Najeriya

'Yan sanda sun kama wanda ya shirya harin bama bamai na 2015 a Abuja

Daya daga cikin wuraren da aka kai hare-haren bama-bamai a garin Abuja cikin watan Oktoba na shekarar 2015.
Daya daga cikin wuraren da aka kai hare-haren bama-bamai a garin Abuja cikin watan Oktoba na shekarar 2015. AFP/File

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da kama daya daga cikin manyan jagororin mayakan Boko Haram a birnin Legas a ranar Alhamis 20 ga watan Disamba.

Talla

Sanarwar ‘yan sandan ta ce an kama Umar AbdulMalik ne tare da wasu ‘yan kungiyar ta Boko Haram bakwai, wadanda ta ce su ne suka jagoranci harin ta’addancin da ya hallaka akalla mutane 18 cikin watan Oktoban 2015, a Kuje da kuma tashar mota ta Nyanya da ke garin Abuja.

A shekarar 2014 ma dai an taba kai hari har sau biyu kan tashar motocin ta Nyanya da ke tashi daga Abuja zuwa gabashin Najeriya.

Hari na farko an kai shi ne a ranar 14 ga watan Afrilu  na 2014, wanda ya hallaka mutane akalla 75, yayin da aka kai hari na biyu a ranar 1 ga watan Mayu na shekarar, inda mutane 16 suka rasa rayukansu.

Rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta kara da cewa Umar Abdulmalik da sauran takwarorinsa, sun kuma amsa cewa su ne wadanda suka tseratar da sama da fursunoni 100 daga gidan yarin Kuje, da kuma kashe jami’an yan sanda 7 a watan Yuli, hadi da aikata fashi a bankuna da dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI