Muhammad Mustapha Mai Kanuri kan ware naira bilyan 55 don raya yankin arewa maso gabas da Boko Haram ta lalata.

Sauti 03:19
Wasu jami'an sojin Najeriya, yayin sintiri a garin Maiduguri da ke jihar Borno.
Wasu jami'an sojin Najeriya, yayin sintiri a garin Maiduguri da ke jihar Borno. REUTERS/Afolabi Sotunde

Daya daga cikin muhimman batutuwa a kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2019 da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisun kasar a makon da ya gabata, shi ne ware naira bilyan 55 domin fara ayyukan hukumar raya yankin Arewa maso gabas da ya samu mummunan koma-baya sakamakon hare-haren Boko Haram.Kan wannan mataki Alhaji Muhammad Mustapha Mai Kanuri, ya ce ware wadannan kudade abu ne da zai bayar da damar sake gina wannan yanki.