Najeriya

Gwamnatin Sokoto ta bayyana Litinin a matsayin ranar hutu

Tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin Jamhuriya ta biyu Alhaji Shehu Shagari.
Tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin Jamhuriya ta biyu Alhaji Shehu Shagari. Reuters/Akintunde Akinleye

Gwamnatin Sokoto ta bayyana Litinin a matsayin ranar hutu domin alhinin rasuwar tsohon shugaban Najeriya Marigayi Alhaji Shehu Usman Shagari, wanda aka yi jana’izarsa ranar Asabar, a karamar hukumar Shagari da ke jihar.

Talla

Jana’izar ta gudana a karkashin jagorancin tsohon shugaban jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto Farfesa Shehu Galadanchi da misalin karfe uku da rabi na yammacin ranar ta Asabar.

Zalika shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin sassauto da tutar kasar, zuwa kasa na tsawon kwanaki uku, domin girmama tsohon shugaban kasar na zamanin mulkin Jamhuriya ta biyu.

A ranar Talatar da ta wuce aka kai tsohon shugaban garin Abuja domin duba lafiyarsa, a ranar Juma’ar nan kuma ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 93.

Marigayi Alhaji Shehu Shagari wanda shi ne Turakin Sokoto ya yi mulkin Najeriya tsakanin shekara ta 1979 zuwa 1983, inda ya kasance shugaban Najeriya na 6.

Tsohon shugaban ya yi malamin makaranta kafin shiga harkokin siyasa a shekara ta 1951, daga bisani aka zabe shi a matsayin dan Majalisar Wakilai a shekara ta 1954.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI