Najeriya

Sojoji sun kai samame ofishin jaridar Daily Trust

Wani bangare na harabar gidan jaridar Daily Trust a Najeriya.
Wani bangare na harabar gidan jaridar Daily Trust a Najeriya. Daily Trust

Rahotanni daga Najeriya sun ce jami’an sojin kasar sun yi wa ofishin jaridar Daily Trust da ke garin Abuja kawanya, inda suka karbe wayoyin hannu da kuma komfutocin tafi da gidanka da ke ofishin jaridar.

Talla

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa, a garin Maiduguri, sojoji, tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaron, sun tsare editan jaridar ta Daily Trust na yankin arewa maso gabashin Najeriya, Uthman Abubakar da kuma wakilinta Ibrahim Sawab.

Babu dai karin bayani kan dalilin daukar matakin da sojojin suka yi, sai dai wata majiyar jaridar ta Daily Trust ta shaidawa AFP cewa, hakan na da nasaba da wani rahoto da jaridar ta wallafa kan halin da ake ciki kan ayyukan sojojin Najeriyar a yankin arewa maso gabashin kasar.

A ranar 31 ga watan Disamba, jaridar ta Daily Trust ta rawaito cewa, mayakan Boko Haram sun kwace iko da wasu yankunan jihar Borno guda 6, ciki har da garin Baga. Sai dai rahoton ya ci karo da sanawar rundunar sojin kasar da ta musanta cewa akwai wasu yankuna da a yanzu ke karkashin ikon mayakan na Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI