Isa ga babban shafi
Najeriya

Zan haramta maida tubabbun Boko Haram cikin jama'a - Atiku

Dan takarar shugabancin Najeriya na babbar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar.
Dan takarar shugabancin Najeriya na babbar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar. AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai gamsu da matakin sakin tubabbun mayakan Boko Haram da sake shigar da su cikin jama’a ba, matakin da ya ce zai haramta idan yayi nasarar lashe zaben 2019.

Talla

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar cikin karshen mako a Abuja ta hannun kakakinsa Paul Ibe.

Dan takarar na jam’iyyar PDP, ya kuma goyi bayan bukatar da dattawan jihar Borno suka mikawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ta neman dakatar da sake hada sauran jama'a da mayakan Boko Haram suka tuba, yayin ziyarar da suka kai masa a baya bayan nan.

A cewar Atiku akwai bukatar a sake nazari mai zurfi kan matakin hade tubabbun ‘yan tada kayar bayan da sauran jama’a, la’akari da yadda wani kwamandan mayakan da aka kama a baya Abba Umar, ya sha alwashin sake komawa cikin kungiyar ta Boko Haram, muddin ya samu damar hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.