Isa ga babban shafi
Najeriya

Gurfanar da Alkalin alkalai ya janyo cece-kuce a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Alkalin alkalan kasar, mai shari'a Walter Onnoghen
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Alkalin alkalan kasar, mai shari'a Walter Onnoghen lailasnews
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tare da zargin ta da yunkurin rage wa bangaren shari’a karsashi a daidai lokacin da ke shirin gudanar da zaben 2019.

Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da Kotun Ladabtar da Ma’aikata ta bukaci Alkalin alkalai, mai shari’a Walter Onnoghen da ya bayyana a gabanta a ranar Litinin domin amsa tambayoyi kan zargin da ake yi masa na cin hanci da rahawa.

Ana zargin Onnoghen da kin bayyana kadarorin da ya mallaka, yayin da zai amsa tambayoyi kan tuhume-tuhume guda shida.

Dokar Najeriya ta bukaci manyan ma'aikatan gwamnati da su bayyana kadarorinsu gabanin darewa da kuma  bayan sauka daga mukamansu.

Ana zargin Alkalin alkalan da kin bayyana kudadensa a asusun da yake ajiyar Dalar Amurka da kuma wanda yake ajiye takardar kudin Pam na Ingila.

Tuni dai, wannan dambarwa ta dauki hankula matuka, in da gwamnonin yankin Kudu maso Kudancin Najeriya, suka bukaci Onnoghen da ya kaurace wa kotun ko kuma ya yi murabusa daga kujerarsa.

Sai dai wasu masana shari’a a Najeriya sun ce, babu wani mahaluki da ya fi karfin tuhuma a kasar muddin ana zargin sa da cin hanci da rashawa, illa shugaban kasa da mataimakinsa da kuma gwamna da mataimakinsa da ba za a tuhume su ba har sai bayan sun sauka daga mukamansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.