Isa ga babban shafi
Najeriya

Obasanjo ya zargi Buhari da yunkurin magudin zabe

Obasanjo da Buhari
Obasanjo da Buhari nationaldailyng.com

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya zargi shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari da shirin tafka magudi a babban zaben da ke tafe cikin watan Fabairu, yayin da ya ce, Boko Haram ta fi samun karfi a yanzu.

Talla

Obasanjo ya bayyana zargin ne cikin wata wasika da ya raba wa manema labarai a birnin Abeokuta, in da ya ce, shugaba Buhari ya dauki salon murdiya irin na tsohon shugaban kasa a mulkin soja, marigayi Sani Abacha.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren martanin jam’iyyun APC da PDP akan wasikar Obasanjo.

Martanin APC da PDP kan wasikar Obasanjo

Obasanjo ya ce, matsalar tsaro ta tabarbare domin kuwa ana ci gaba da garkuwa da mutane a sassa daban daban na kasar, baya ga kungiyar Boko Haram da ya ce, tafi samun karsashi a yanzu.

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa, muddin ‘yan Najeriya suka ki kawar da Buhari daga kujerar mulki a zaben watan gobe, to Boko Haram za ta mamaye daukacin yanki kudancin Afrika, abin da zai jefa rayuwar jama cikin hadari a cewarsa.

Tuni fadar shugaba Buhari ta mayar wa Obasanjo martani a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bukace shi da ya je gaban kwararren likita domin duba lafiyarsa, sannan ta yi masa fatan samun lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.