Najeriya

Ezekwesili ta janye daga takarar shugabancin Najeriya

'Yar takarar neman shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar adawa ta ACPN Obiageli Ezekwesili.
'Yar takarar neman shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar adawa ta ACPN Obiageli Ezekwesili. REUTERS/Afolabi Sotunde

‘Yar takarar kujerar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar ACPN, Obiageli Ezekwesili ta sanar da janye takararta.

Talla

Ezekwesili ta ce a yanzu za ta maida hankali wajen kulla wani kawance mai karfi tsakaninta da wasu jam’iyyu, domin hana jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP samun nasara a zaben da zai gudana na ranar 16 ga watan Fabarairu.

‘Yar takarar ta ACPN ta ce ba ta dauki matakin janye takararta ba, sai da ta tuntubi masana da ke ciki da wajen Najeriya.

Kafin janyewar Ezekwesili daga zaben na 2019, yawan ‘yan takarar da za su fafata a zaben shugabancin na Najeriya ya kai 72, inda a yanzu ya koma 71.

Masu iya magana dai sun ce “ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare” domin lokaci ne kawai zai nuna ko kawancen da Ezekwesili za ta kulla da wasu jam’iyyun zai yi nasarar kayar da APC mai mulki, da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben shugabancin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI