Najeriya

Najeriya ta gargadi kasashen ketare kan yi mata katsalandan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Amurka Donald Trump.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da takwaransa na Amurka Donald Trump. Reuters/Carlos Barria

Gwamnatin Najeriya ta gargadi kasashen ketare da su kaucewa yin katsalandan kan al’amuran da suka shafi kasar, wanda ka iya haifar da rudani, rashin yadda da juna tsakanin ‘yan Najeriya, da kuma haifar da shakku kan sahihancin zabukan kasar.

Talla

Gargadin na kunshe cikin sanarwar da kakakin gwamnatin Najeriyar Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja.

Gwamnatin Najeriya dai ta maida martani ne kan tsokacin da wasu kasashen ketare da suka hada da Amurka Birtaniya da kuma kungiyar EU suka yi, kan matakin shugaban kasar Muhammadu Buhari, na dakatar da Alkalin Alkalai mai shari’a Walter Onnoghen, tare da nada Mai shari’a Ibrahim Tanko a matsayin mukaddashi.

Sanarwar ta yi amfani da kakkausan harshe wajen sukar duk wani yunkurin yin katsalandan kan al’amuran Najeriya da kai iya rura wutar sabani tsakanin ‘yan kasar ko kuma haddasa rashin yadda da tsarin dimokaradiyar da take kai.

Majalisar dattijan Najeriya dai, ta tsaida Talata mai zuwa, a matsayin ranar da za ta tattauna kan matakin bangaren zartarwa na dakatar da Onnoghen.

Shugaban majalisar dattijan Bukola Saraki, wanda ya bukaci zaman na musamman a ranar Talatar, ana sa ran ganawarsa da sauran jagororin majalisar a ranar Lahadi.

Ranar Juma’ar da ta gabata Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya dakatar da alkalin alkalai Walter Onnoghen, har sai an kammala yi masa shari’a kan zargin kin bayyana wasu kadarori da ya mallaka, cikin har da kudaden kasashen ketare a asusunsa, inda aka maye gurbinsa da mai shari’a Ibrahim Tanko a matsayin mukaddashin alkalin alkalan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI