Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta maida martani kan rahoton Amnesty

Wasu sojin Najeriya a Gamboru Ngala, dake jihar Borno.
Wasu sojin Najeriya a Gamboru Ngala, dake jihar Borno. REUTERS/Afolabi Sotunde

Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da rahoton kungiyar Amnesty International, da ya ce mayakan Boko Haram sun hallaka mutane 60 a wani hari da suka kai kan garin Rann da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno.

Talla

Mataimakin daraktan yada labaran rundunar musamman ta Operation Lafiya Dole da ke Yakar Boko Haram, Kanal Onyema Nwachukwu ne ya fitar da sanarwar a garin Maiduguri.

A ranar Juma’ar da ta gabata Amnesty International ta wallafa rahoton cewa tana da shaidun hotunan tauraron da adam da ke nuna cewa mayakan na Boko Haram a ranar 28 ga watan janairu, sun hallaka rayuka 60 da kuma kone gidaje da dama, biyo bayan janyewar dakarun sojin da ke baiwa yankin tsaro.

Sai dai a martaninta, rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan na Boko Haram sun kai hari kan garin na Rann a ranar 14 ga watan Janairu, ba 28 ga watan ba, zalika a waccan lokacin dakarun Najeriya sun tarwatsa aniyar maharan, inda suka kashe ‘yan kunar bakin wake 2 da wasu mayakan 3, sauran kuma suka tsere dauke da raunukan harbi.

Rundunar sojin ta kara da cewa tuni dakarunta suka kaddamar da farmakin kakkabe wuraren da mayakan na Boko Haram ke amfani da su a matsayin maboya a kauyukan da ke zagaye da garin na Rann, kuma sun yi nasarar lalata sansanonin mayakan da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI