Dole mu binciki Obasanjo kan batan dala biliyan 16 - Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin gudanar da bincike kan dalar Amurka biliyan 16, da gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ta ce ta kashe wajen wadata ‘yan Najeriya da hasken wutar lantarki.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaba Buhari, wanda ya sha alwashin a ranar Talata yayin yakin neman zabensa garin Yenagoa na jihar Bayelsa, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa an kwato biliyoyin dalolin da wasu suka yi kwanciyar magirbi a akansu, su kuma fuskanci hukunci.
A tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 gwamnatin tsohon shugaba Obasanjo, ta bayyana kashe dala biliyan 16 kan inganta samar da hasken lantarki a Najeriya, sai dai har yanzu ana fuskantar kalubalen rashin wutar a sassan kasar.
Jim kadan bayan alwashin na shugaban Najeriya, manema labarai suka tuntubi kakakin tsohon shugaba Obasanjo dangane da lamarin, Kehinde Akinyemi, wanda ya ce sun dade yana sauraron ranar da binciken zai soma, zalika tun a shekarar bara, tsohon shugaban ya bayyana cewa a shirye yake da ya amsa tambayoyi kan zargin.
A watan Yunin shekarar 2018, Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da shirye-shiryen kama shi akan zarge-zargen karya domin haramta mishi fadin albarkacin bakinsa.
Sanarwar da shugaban ya fitar ta hannun kakakinsa, Kehinde Akinyemi, ta zargi Buhari da yunkurin yin amfani da takardu, da kuma shaidun karya wajen tuhumarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu