Najeriya-Lassa

Cutar Lassa na ci gaba da kisa a Najeriya

Fiye da Mutane 300 kawo yanzu aka tabbatar da sun kamu da cutar ta Lassa cikin kasa da mako biyu a jihohin Najeriyar
Fiye da Mutane 300 kawo yanzu aka tabbatar da sun kamu da cutar ta Lassa cikin kasa da mako biyu a jihohin Najeriyar barbaric.com

Hukumar da ke kula da cutuka masu saurin yaduwa a Najeriya NCDC ta sanar da karuwar mutane 37 da suka kamu da cutar Lassa cikin kasa da mako guda a sassan kasar.

Talla

A jawabansa babban jami’in hukumar, Chikwe Ihekweazu, ya ce mutanen 37 sun kamu da cutar ta Lassa ne daga ranar 4 zuwa 10 ga watan nan na Fabarairu.

Mr Ihekweazu ya ce a gwajin da suka gudanar daga ranar 1 zuwa 10 ga watan nan kan mutane 947 daga jihohi 20 da ake kyautata zaton su na dauke da cutar sun tabbatar da cutar a jikin mutane 324.

Babban jami’in ya nuna cewa, tun bayan sake barkewar cutar a farkon shekarar nan ta 2019 akalla mutane 69 ta hallaka a jihohin Najeriyar 20.

Babban jami’in hukumar, ta NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce daga ranar 8 ga wata mutane 57 ne suka mutu sanadiyyar cutar, amma kawo yanzu adadin ya karu zuwa 69 matakin da ke nuna cewa cutar na ci gaba da yaduwa a sassan Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.