Najeriya

INEC ta musanta bacewar muhimman takardun zaben gwamna a Zamfara

Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC.
Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC. REUTERS/Nyancho NwaNri

Hukumar shirya zaben Najeriya INEC a Zamfara, ta musanta zargin da wasu jam’iyyu a jihar suka bayyana, na sace wasu takardun rubuta sakamakon kuri’un da za a kada a zaben gwamnoni da ke tafe.

Talla

Garba Galadima, shugaban sashin ilimintar da masu kada kuri’a da yada labaran hukumar ta INEC reshen jihar ta Zamfara, ya bayyana zargin a matsayin kagen da babu kamshin gaskiya a cikinsa.

A cewar Galadima, sai a ranar 6 ga watan Maris da muke ciki, INEC za ta gayyaci baki dayan jami’anta na kananan hukumomin jihar 14, domin mika musu muhimman kayayyakin zabukan gwamna da na ‘yan majalisun jihohi, da zai gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Jami’in na INEC ya kara da cewa, hukumar za ta gayyaci dukkanin wakilan jam’iyyu hadi da ‘yan takararsu na gwamna, domin shaida yadda za a rarraba kayayyakin zaben, domin tantance gaskiya ko akasin zargin rufarufa da ake musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.