Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben Gwamnoni ba zai gudana a jihohi 7 ba

Wasu 'yan Najeriya yayin dakon soma kada kuri'a a zabukan kasar na 2019.
Wasu 'yan Najeriya yayin dakon soma kada kuri'a a zabukan kasar na 2019. REUTERS/Nyancho NwaNri
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Yayin da ake gudanar da zaben Gwamnonin Jihohi 29 a fadin Najeriya, hukumar zaben kasar INEC, tace zaben ba zai gudana a Jihohin kasar guda 7 ba, saboda har yanzu wa’adin Gwamnonin dake karagar mulki bai kare ba.

Talla

Jihohin da zaben kujerun Gwamnan ba zai gudana ba sun hada da Kogi, Osun, Ondo, Anambra, Ekiti da kuma Edo.

Sai dai hukumar zaben tace za’a gudanar da zaben kujerun ‘yan majalisu a baki dayan Jihohin kasar guda 36.

A mukaman Gwamna 29 da ake fafatawa, hukumar INEC ta ce ‘yan takara dubu 1, da 68 ke fafatawa, yayinda a matakin ‘yan majalisun jihohi guda 991 ake da jimillar ‘yan takara dubu 14 da 583 a jihohi 36.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.