Najeriya

Zaben Gwamnoni bai kammala ba a Filato, Sokoto, Bauchi, da Adamawa

Wasu ma'aikatan hukumar zaben Najeriya INEC, yayin aikin tattara sakamakon kuri'un da aka kada a zabukan kasar.
Wasu ma'aikatan hukumar zaben Najeriya INEC, yayin aikin tattara sakamakon kuri'un da aka kada a zabukan kasar. AP

Hukumar Zaben Najeriya ta bayyana zaben Gwamnonin Jihohin Plateau, Bauchi, Sokoto da Adamawa a matsayin wadanda basu kammala ba.

Talla

A Jihar Plateau, Baturen zaben Farfesa Richard Anande, yace Jam’iyyar APC ke kan gaba da kuri’u 583,255, yayin da PDP ke da 538,326, wanda ya nuna banbancin 44,929.

Farfesa Bande wanda yace an soke kuri’u 49,377 wadanda kan iya sauya alkaluman zaben, saboda haka doka tace sai an sake zabe a wadannan wurare da aka soke sakamakon su.

A Jihar Bauchi, Baturen zabe Farfesa Muhammed Kyari yace za’a sake zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa, saboda matsalolin da aka samu a wasu tashoshin zabe.

Kafin hakan dai, Farfesa Kyari yace Jam’iyyar PDP ke kan gaba da kuri’u 469,512, yayin da APC ke da 465,453.

A Jihar Sokoto, Baturen zabe Farfesa Fatima Batul Mukhtar ta sanar da cewar Jam’iyyar PDP ke gaba da kuri’u 489,558, yayin da APC ke da kuri’u 486,558, kana kuma an soke kuri’u 75,403, wanda adadin su kan iya sauya sakamakon zaben, dan haka tilas za sake kada kuri’u a inda aka soke na baya.

A Adamawa, hukumar zaben Najeriya ta bayyana cewa zaben Gwamnan Jihar Adamawa da aka yi a karshen mako ba, bai kammala ba, saboda matsalolin da aka samu a wasu tashoshin zabe 44 wanda sakamakonsu zai iya sauya alkaluman zaben baki daya.

Kafin dai bayyana zaben a matsayin wanda bai kamala ba, wakilinmu Ahmad Alhassan ya shaida mana cewar Jam’iyyar PDP ke gaba da kuri’u 367,471, sai APC 334,995, sai ADC mai 113,205.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.