Najeriya

Shaidu sama da 400 za su kalubalanci nasarar Buhari a Kotu - PDP

Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar.
Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar. REUTERS/Nyancho NwaNri

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana tattara shaidu sama da 400 da zai yi amfani da su a kotun sauraron kararrakin zabe, wajen kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabarairu, wanda shugaban Najeriya mai ci Muhammadu Buhari ya lashe.

Talla

Mai baiwa jam’iyyar PDP shawar kan shari’a Mista Emmanuel Enoidem ne ya wakilci Atiku wajen bayyana shigar da karar kalubalantar zaben shugabancin Najeriyar, yayin ganawa da manema labarai a harabar kotun daukaka kara da ke Abuja.

Mista Enoidem ya kara da cewa, manyan lauyoyi masu lambar girmamawa ta SAN guda 20 ne za su tsayawa dan takarar jam’iyyar adawar ta PDP.

Wakilinmu daga Abuja Muhammadu Kabiru Yusuf, ya aiko mana da rahoto akai.

Shaidu sama da 400 za su kalubalanci nasarar Buhari a Kotu - PDP

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI