Najeriya-Kano

Gwamnatin Kano na ci gaba da yin manyan ayyuka a mazabar Gama

Sabuwar hanyar da ake shimfidawa a Titin Audu Utai da ke mazabar Gama a Kano.
Sabuwar hanyar da ake shimfidawa a Titin Audu Utai da ke mazabar Gama a Kano. Premium Times Nigeria

Rahotanni daga Kano a Najeriya, sun tabbatar da cewa, gwamnatin jihar a karkashin Abdullahi Umar Ganduje, ta jajirce wajen gudanar da wasu ayyukan samar da ababen more rayuwa, ga al’ummar mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa.

Talla

Manyan ayyukan da Gwamnatin jihar ta Kano ke aiwatarwa, sun hada da gina hanya, kwashe tarin shara da ta shafe tsawon lokaci a jibge da kuma haka rijiyoyin birtsatsai.

‘Yan siyasa, masu sharhi da sauran jama’a suka soma tofa albarkacin bakinsu akan matakin na Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Yayinda magoya bayansa ke kare ayyukan da cewa bisa kyakkyawar niyya aka kaddamar da su, a bangare guda ‘yan adawa na ci gaba da ikirarin cewa, tilas ce ta sa gwamnatin Jihar ta Kano kaddamar da ayyukan farantawa al’ummmar ta Gama, la’akari da cewa mazabar ke kan gaba wajen jagorantar yadda sakamakon karshe na zaben kujerar Gwamna da za a karasa a ranar Asabar 23 ga Maris zai kaya, saboda yawan al’ummar yankin.

Sai dai tuni Gwamnan jihar ta Kano ya musanta cewa yana gudanar da manyan ayyukan ne domin al’ummar mazabar su kada masa kuri’a a zaben da za a karashe.

Mazabar Gama dai na daga cikin mazabun da aka soke kuri’un da aka kada a zaben kujerar Gwamna da ya gudana a ranar 9 ga watan Maris sakamakon saba ka’idar dokr zabe, ta hanyar kokarin haddasa tashin hankali yayin aikin zaben.

Soke kuri’un da aka kada a mazabar ta Gama dai ya biyo bayan yunkurin haifar da rikici a cibiyar tattara sakamakon zaben Gwamna da ke mazabar a karkashin jagorancin wasu manyan jami’an gwamnatin jihar Kano da nufin dakatar da aikin tattara sakamakon kuri’un da aka kada, inda kuma suka yi nasarar lalata takardar da ke dake da sakamakon, a ranar 11 ga watan Maris.

A waccan lokacin manyan jami’an Gwamnatin jihar ta Kano da suka bayyana a cibiyar tattara sakamakon da ke mazabar ta gama sun hada da mataimakin Gwamna, Nasiru Gawuna, Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo da kuma shugaban karamar hukumar ta Nasarawa Lamin Sani.

Dan takarar jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya baiwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tazarar kuri’u dubu 26, sai dai saboda kuri’u dubu 141 da aka soke, hukumar INEC ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, la’akari da cewa da yawansu kuri’un ya zarta tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takarar guda biyu.

Ranar Asabar 23 ga watan Maris, 2019, za a karsa zaben kujerar Gwamnan ta jihar Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.