Najeriya

'Yan bindiga sun bukaci naira miliyan 300 kan Sheikh Ahmad Suleiman

Shiekh Ahmad Suleiman.
Shiekh Ahmad Suleiman. YouTube

Rahotanni daga Najeriya sun ce masu garkuwa da mutane sun bukaci a basu naira miliyan 300 domin sakin fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Suleiman da ya kwashe kwanaki a hannun su.

Talla

A daren ranar Alhamis ta makon da ya gabata, ‘yan bindigar suka sace Shiekh Ahmad Suleiman, tare da wasu mutane biyar, a jihar Katsina.

Rahotanni sun ce Malamin da sauran wadanda ke tare da shi, na kan hanyarsu ta Komawa Kano ne daga jihar Kebbi, inda ‘yan bindigar suka sace su a daren ranar Alhamis akan hanyar Sheme zuwa Kankara.

Dangane da bukatar kudin Fansar ne muka tuntubi shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, kan halin da ake ciki, wanda yace suna kan kokari samun nasarar yantar da Shiekh Ahmad Suleiman, kuma sun kan tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da Malamin.

Dangane da halin da Malamin ke ciki, Shiekh Abdullahi Bala Lau ya yana cikin koshin lafiya domin yana ganawa da iyalansa, illa kawai fargabar da yake ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI