Najeriya

APC da PDP na rububin lashe kujeru a zaben Gwamna

Yau ne Hukumar Zaben Najeriya ke gudanar da karashen zaben Gwamna a wasu mazabu na jihohin kasar, in da gwamnonin da ke kan karaga ke fafatawa da abokan hamayyarsu da ke neman kawar da su daga madafun iko.

Tuni jama'a da dama suka dauki haramar kada kuri'unsu a mazabun da ake gudanar da karashen zaben Gwamnoni a wasu jihohin Najeriya
Tuni jama'a da dama suka dauki haramar kada kuri'unsu a mazabun da ake gudanar da karashen zaben Gwamnoni a wasu jihohin Najeriya guardian.ng
Talla

Jihohin da ake gudanar da karashen zaben sun hada da Kano da Sokoto da Filato da Benue da kuma Bauchi  bayan Hukumar INEC ta bayyana zaben jihohin a matsayin wadanda ba su kammala a ranar 9 ga wannan wata na Maris.

Kodayake INEC ta ce, za ta gudanar da karashen zaben a jihohi 18, amma hankula sun fi karkata a wadannan jihohin da aka lissafa, yayinda kotu ta bayar da umarnin dakatar da zaben a jihar Adamawa

Jam’iyyar APC na fatan karbe kujerun gwamnonin jihohin Sokoto da Benue, yayinda PDP ke kokarin ganin ta karbe Kano da Filato da kuma Bauchi.

Wadannan jihohin na da matukar muhimmanci a siyasar Najeriya saboda yawan al’ummominsu da kuma kuri'un da suke bayarwa, abinda ya sa jam’iyyun kasar ke fatan lashe su.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci al'ummar mazabun da ake gudanar da zaben da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri'u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI