Isa ga babban shafi
Najeriya

Yadda karashen zaben Gwamna ya gudana a wasu jihohin Najeriya

Wani jami'in hukumar zaben Najeriya INEC, rike da takardar zabe.
Wani jami'in hukumar zaben Najeriya INEC, rike da takardar zabe. eNCA
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 min

Rahotanni daga Bauchi a tarayyar Najeriya, sun ce karashen zaben kujerar Gwamna ya gudana cikin kwanciyar hankali, da kuma tsauraran matakan tsaro a mafi akasarin sassan da zaben ya gudana.

Talla

Sai dai gungun wasu mutane dauke da makamai sun sace jami’an hukumar zabe guda 4.

Lamarin dai ya auku ne a wata rumfar zabe da ke karamar hukumar Jam’are, inda wani jami’in hukumar zaben da ya tsira, ya ce gungun mutanen sun zo ne cikin motoci hilux 7, inda suka tarkata jami’an na INEC hudu da sauran kayan zabe sukai awon gaba da su.

Kawo yanzu kuma babu karin bayani daga gwamnatin jihar ko hukumar ‘yan sanda.

A Jihar Sokoto inda a nan ma ake gudanar da karashen zaben na Gwamna, wakilinmu ya rawaito cewa mutane da dama sun kada kuri’a cikin kwanciyar hankali, sai dai fa an samu hargitsi a wasu sassan jihar, ciki har da rumfar zabe ta Sarkin Adar Kwanni da ke cikin gari, da cikin garin Kedde, amma daga bisani jami’an tsaro sun maido da doka da oda, an kuma ci gaba da kada kuri’a.

A Filato, kwamishinan ‘yan sandan Jihar Isaac Akinmoyode, ya shaidawa manema labarai cewa karashen zaben na gudana cikin kwanciyar hankali. Zalika wakilinmu da ke jihar ya tabbatar da rahoton cewa ba’a fuskanci tashin hankali ba.

A jihar Bayelsa kuwa, hukumar zaben Najeriyar INEC ta dakatar da kada kuri’a a mazaba guda daga cikin uku da karashen zaben na gwamna ke gudana, sakamakon umarnin yin hakan da kotu ta bada.

Shugaban hukumar zaben a jihar ta Bayelsa, Mista Monday Udoh ya ce umarnin ya shafi mazabar Brass ce ta daya, amma a sauran mazabun da suka hada da Ogbia ta 2 da Souther-Ijaw komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.