Najeriya

APC ta doke PDP a zaben Gwamnan Filato

Gwamnan Filato da ke kan mulki Simon Bako Lalong na Jam’iyyyar APC, ya sake lashe zaben kujerar tasa bayan karasa zaben da INEC ta bayyana a matsayin wanda bai kammala ba a makon da ya gabata.

Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong.
Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong. Premium Times Nigeria
Talla

Simon Lalong ya lashe zaben ne da yawan kuri’u dubu 595,582, abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP kuma Sanata Jeremiah Useni, ya samu kuri’u dubu 546,813.

Sakamakon ya tabbata ne bayan gudanar da karashen zaben Gwamnan jihar ta Filato, a rumfunan zabe 40 da ke kananan hukumomi 9.

Sakamakon karashen zaben dai ya nuna cewa Gwamna Lalong ya samu kuri’u dubu 12,327, yayinda Useni na PDP ya samu kuri’u dubu 8,487.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI