Najeriya

Tsarin "Inconclusive" ya kyautata sahihancin zaben Najeriya - INEC

Wani jami'in hukumar zaben Najeriya INEC, yayin kidayar kuri'u a garin Lagos.
Wani jami'in hukumar zaben Najeriya INEC, yayin kidayar kuri'u a garin Lagos. REUTERS/Adelaja Temilade

Hukumar zaben Najeriya, ta hannun kwamishinanta na kasa mai lura da jihohin Kano, Katsina da Jigawa, Abubakar Nahuce, ta ce tsarin sake gudanar da zabuka bayan bayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba wato “Inconclusive a turance” ya taimaka wajen kyautata sahihancin zabuka a kasar.

Talla

Abubakar Nahuce ya bayyana haka ne a wannan Juma’a yayin mika takardar shaidar samun nasarar lashe zabe, ga Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari.

Nahuce yace tsarin sake gudanar da zabuka a wuraren da basu kammala ba, saboda fuskantar matsaloli na saba ka’ida ko hatsaniya, ya taka rawa wajen rage tazara mai nisa da aka saba samu, tsakanin wanda ya lashe zabe da mai biye da shi, kamar yadda aka gani a jihohin Sokoto da Adamawa.

Tsarin "Inconclusive" na sake zabuka a wuraren da aka fuskanci matsalolin kada kuri'a ya haifar da muhawara tsakanin 'yan Najeriya, inda wasu ke goyon bayan tsarin a matsayin hanyar kwatowa wandanda aka murdewa sakamakon hakkinsu, yayinda wasu ke kallon tsarin a matsayin wata sabuwar hanyar sauya gaskiyar lamarin na sakamakon kuri'un da aka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.