Najeriya

'Yan bindiga sun kashe manoma a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu satar shanu da garkuwa da jama’a ne a arewacin Najeriya, sun kashe manoma akalla 10 a jihar Zamfara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta tabbatar.

Jihar Zamfara na fama da hare-haren barayin shanu
Jihar Zamfara na fama da hare-haren barayin shanu shakarasquare
Talla

‘Yan bindigar haye akan barura, sun kai farmakin a wata gonar albasa da ke kauyen Kwari na Shinkafi, in da suka harbe manoman da ke bakin aiki kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya bayyana.

Mohammed ya ce, sun baza jami’an tsaro domin maido da zaman lafiya a yankin, amma bai yi karin bayani kan musabbabin harin ba, amma ana ganin hakan bai rasa nasaba da harin ramako, lura da cewa, a ‘yan kwanakin nan ne, sojoji suka fatattaki barayin shanun daga maboyarsu.

Makwanni biyu kenan da sojojin suka kai samame a sansanonin ‘yan bindigar, in da suka hallaka kwamandojinsu kamar yadda wani mazaunin kauyen Kwari, Hashimu Abu ya ce.

Jihar Zamfara na fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke kashe jama’a babu kakkautawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI