Najeriya

Dole PDP ta kakkabe munafukai don dawo da kimarta- Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, ya zama tilas jam’iyyar PDP ta kakkabe munafukai da baragurbin mambobi kafin ta maido da martabarta.

Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo Getty Images
Talla

Tsohon shugaban ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar da su yi zawarcin mutanen da ya kira “ jama’a masu mihimmanci tsakanin  da za su bayar da gudunmawa duk wuya duk runtsi".

Obansanjo ya bayyana haka ne a yayinda wata tawagar shugabannin PDP daga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ta ziyarce shi a gidansa da ya gina hade da katafaren dakin karatunsa da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Obasanjo ya ce, da dama daga cikin shugabannin na PDP na cika aljihunsu da tubinsu ne kawai, yana mai cewa, gurbatattun mambobinta ba su da jajircewar maidowa da kungiyar martabar da ta rasa.

Har ila yau, tsohon shugaban ya kara da cewa, Najeriya na bukatar kwakkwarar murya 'yan adawa a PDP da zummar gina demokradiya mai karfi a kasar.

"Najeriya ba za ta ci gaba ba muddin muka ci gaba da tafiya kan turbar da muke kai a yanzu." inji nObasanjo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI