Najeriya

"Wa'adin nisan-kwana a Najeriya bai wuce shekaru 55 ba"

Hukumar Kula da Yawan Al’umma ta Najeriya ta bayyana shekaru 55 da watanni biyu a matsayin tsawon wa’adin nisan-kwana da ake sa ran ‘yan kasar za su rika kaiwa kafin mutuwa ta riske su.

Wasu 'yan Najeriya da ke zirga-zirga a birnin Lagos mai cike da hada-hadar kasuwanci
Wasu 'yan Najeriya da ke zirga-zirga a birnin Lagos mai cike da hada-hadar kasuwanci Premium Times Nigeria
Talla

Mukaddashin shugaban hukumar ta NPC, Hassan Bashir ya bayyana haka a birnin New York na Amurka a yayin gabatar da jawabi kan Najeriya a taron Hukumar Kula da Yawan Al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya karo na 52.

Bashir ya ce, wa’adin shekaru 60 ko fiye haka na nisan-kwana a Najeriya da aka sani a can baya, a yanzu ya takaita ne akan kasa da kashi 5 cikin 100 na daukacin al’ummar kasar.

Jami’in ya kara da cewa, kashi 63 na jama’ar kasar matasa ne da shekarunsu bai wuce 25 ba, yayinda ‘yan kasa da shekaru 15 ke da kashi 42.

A bangare guda, kashi 50 na matan da ake da su a kasar, za su iya haihuwa domin basu wuce shekarun daukan ciki ba.

Sai dai ya ce, alkaluman da suka tattara a bara, sun nuna cewa, har yanzu ana fama da matsalar daukan cikin da ba a shirya masa ba tsakanin ‘yan mata masu shekaru 15 zuwa 19.

A cewarsa, matsalar daukan irin wannan juna biyun, na jefa mata cikin hadarin rasa rayuwa a lokacin naguda ko kuma haihuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI